Gwamnatin jihar Adamawa ta ce ta dawo da ma’aikata 1,699 da gwamnatin da ta shude ta kora daga aiki.
Solomon Kumangar, babban daraktan, yada labarai da sadarwa ga Gwamna Ahmadu Fintiri, ne ya sanar da hakan ga Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) a Yola ranar Litinin din nan.
Ya ce ma’aikatan da abin ya shafa sun kasance malaman batch D 699 wadanda tun da farko aka dauka aka tura su makarantun firamare da sakandare, inda ya ce an mayar da su bakin aiki.
Ya kara da cewa ma’aikatan lafiya 1,000 ne kuma aka mayar da su bakin aiki, inda ya ce an kore su a baya ne saboda rashin tsarin daukar ma’aikata da gwamnatin da ta shude.
“Mun gudanar da bincike mai zurfi don gano abubuwan da ba su dace ba da nufin gyara kuskuren da aka yi a lokacin daukar su saboda ba mu nemi kowa ba,” in ji shi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kumangar ya lura cewa a kwanan baya gwamnatin da ke yanzu ta dauki karin jami’an duba ababen hawa (VIOs) guda 70 domin inganta harkar zirga-zirgar ababen hawa.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/hukumar-nahcon-ta-kammala-jigilar-dawo-da-alhazan-najeriya/
Ya ce wannan shiri zai inganta al’amuran tituna a tsakanin masu ababen hawa da kuma tabbatar da tsaron hanyoyin mota da tabbatar da ingancin ababen hawa da kwazon direbobin da ke bin hanyoyin.
“Hakan kuma zai inganta harkar samar da kudaden shiga na gwamnati ta hanyar samar da bayanan ababen hawa da kuma sanya takunkumi ga masu ababen hawa.”
Ya kara da cewa a kwanakin baya gwamnati ta dauki karin malaman kimiyya 2,000 kuma an tura su makarantun sakandare domin koyar da manyan darussan kimiyya.
Ya bayyana cewa an dauki wannan shiri ne da nufin bunkasa ilimin kimiyya da nufin ganin jihar ta ci gaba da tafiyar da harkokin kimiyya da fasaha a duniya.
“Kwanan nan mun mayar da da yawa daga cikin ma’aikatan gidan gwamnati zuwa ma’aikatan dindindin da masu karbar fansho, maimakon zama na yau da kullun ko yin aiki na wucin gadi.”
Kamfanin sillancin labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin jihar Adamawa ta dauki ma’aikata 1,113 kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya aiki wadanda aka tura yankunan karkara domin fadada ingantaccen tsarin kula da lafiyar da ake da su.
(NAN)
(SOLACEBASE)