Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe wata makaranta mai zaman kanta mai suna Noble Kids Academy da ke Kwanar Dakata a karamar hukumar Nassarawa cikin gaggawa, inda wadanda ake zargin suka binne gawar wata yarinya da suka sace, mai suna Hanifa Abubakar.
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa marigayiyar, yarinya ‘yar shekara biyar, an sace ta ne a watan Nuwamba, 2021, a Kwanar Dakata ta hannun malaminta, Abdulmalik, wanda babban wanda ake zargi da aikata laifin, a cewar ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda suka sace yarinyar daga baya sun bukaci a biya su Naira miliyan 6 domin a sake ta kafin a kashe ta.
Kwamishinan ilimi na jihar, Muhammad Saidu Kiru ne ya sanar da rufe makarantar a ranar Alhamis, bayan da ‘yan sanda sun gano gawar wacce aka binne a makarantar mai zaman kanta.
Da yake bayyana alhininsa kan lamarin, kwamishinan ya ce baya ga rufe makarantar, gwamnatin jihar za ta fara binciken makarantu masu zaman kansu da malaman da ba su yi rajista ba domin duba irin wadannan laifuka.
Ya kuma yi kira ga iyayen da ‘ya’yansu ke shiga makarantar masu zaman kansu da su hana su yin hakan har sai an kammala bincike.