Gwamnatin Jihar Katsina ta ceto wata yarinya
Gwamnan Jihar Katsina ya amshi yarinyar nan mai suna Amina ‘yar asalin karamar hukumar Danmusa da akayi yunkurin aurar da ita ga wani Dan ta’adda.
Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina Haj. Zulaihat Dikko Umar Radda ta amshi Amina a fadar Gwamnatin Jihar, amadadin Gwamnan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da kwamitin da zai biya garatutin shekaru 3
Gwamna Malam Dikko Umar Radda zai rike Amina, a hannunsa tare da kula da rayuwarta da tarbiyarta har illa masha Allahu, yanzu haka za a sanya Amina, a makaranta ta hannun mai baiwa Gwamna shawara akan ilmin ‘ya’ya mata.
Shugaban karamar hukumar Danmusa Hon. Sanusi Abbas Dangi ne ya mika Amina ga Uwar gidan Gwamnan kamar yadda Gwamnan ya ba shi umurnin kawo ta.
In dai za a iya tunawa, labarin Amina ya rakade kafafen sada zumun ta na zamani, a wani faifan bidiyo da wasu ‘yan civilian JTF sukayi hira da ita, a lokacin da su ka hadu da ita tana kokarin guduwa,inda ta bayyana masu halin da ta ke ciki na yunkurin aurar da, ita ga wani Dan ta’adda.
A faifan bidiyon Amina ta fada cewa Dan ta’addan ya yi barazanar kashe wadanda ke rike da ita ma damar su ka hana shi aurenta, hakan yasa su ka tsorata sukayi yunkurin aurar da ita gareshi, ita kuma taki amincewa ta gudu, inda tace ta gwammace ta shiga duniya da ta aure shi.