Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna KADSUBEB ta bayyana cewa, ta shirya gudanar da jarabawar daukar malaman makaranta daga ranar 17 zuwa 28 ga watan Oktoba a shiyyoyi uku na jihar
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sanarwar da KADSUBEB ta fitar ta ce za a gudanar da jarrabawar ne a cibiyar fasahar sadarwa ta Kofar Doka, Zariya; Harabar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da ke Kaduna da kuma reshen KASU a Kafanchan, mai wakiltar shiyyar Arewacin jihar, Tsakiya da kuma Kuduncin jihar ta kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kashi 30 Na Yan Najeriya Jahilai Ne – Ministan Ilimi
A watan Yuli, Shugaban Hukumar ta KADSUBEB, Malam Tijani Abdullah, ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci hukumar ta dauki malamai 10,000 a jihar.
A WANI LABARIN KUMA: Ba Ganduje Ke Daukar Nauyin Takarana Na Gwamna Ba– Dan Takarar PRP
Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimakawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin yada labarai, ya karyata rahotannin da ke cewa tsohon maigidansa ne ke daukar nauyin zabensa na gwamna a karkashin jam’iyyar PRP.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi ta tattaunawa a Kano cewa mai yiwuwa gwamnan ne ke da hannu a burin tsohon mai taimaka masa a fannin yada labarai, domin a samu saukin a fafatawa da dan takarar gwamnan Kano a inuwar jam’iyyar APC mai mulki