Gwamnatin jihar Kaduna za ta kashe Naira biliyan 8.2 wajen kula da lafiya a matakin farko a shekarar 2022, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Wannan dai na kunshe ne a cikin kasafin kudi naira biliyan 278.6 da gwamna Nasir El-Rufai ya sanya wa hannu a ranar 22 ga watan Disamba kuma Kamfanin na NAN ta samu a Kaduna ranar Laraba.
Takardar ta nuna cewa daga cikin Naira biliyan 8.2 da aka ware wa Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta jiha (PHCDB), an ware Naira biliyan 5.8 ne don gudanar da manyan ayyuka yayin da Naira biliyan 2.5 za’ayi amfani da su a harkokin yau da kullun.
Haka kuma ya nuna cewa an ware Naira biliyan 4.3 don ginawa, gyarawa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin f farko (PHCs), Wanda suka hadar da asibitoci 255, sake gina hedikwatar hukumar na PHCB da ayyukan tuntuba.
Hakanan, an ware Naira miliyan 233.6 don siyan kayan kariya na mutum don cibiyoyin lafiya 1,154 da rigakafin COVID-19, yayin da aka ware Naira miliyan 25.5 don siyan kayan aiki a cikin asibitoci 255 dake jihar.
An Kuma ware Naira miliyan 954.3 don gudanar da ayyukan kiwon lafiya daban-daban,
Takardar ta ci gaba da nuna cewa, za a kashe Naira miliyan 100 wajen siyan kayayyakin masarufi masu Tasirin Kiwon Lafiyar Jama’a, Masu Tallafawa Ma’aikatan kiwon lafiya (CHIPS) da kuma wayar da kan jama’a.
Haka kuma gwamnati ta ware Naira miliyan 136.6 domin samar da wutar lantarki a asibitoci kula da Lafiya a matakin farkko PHC 255 da aka inganta.
Hakazalika, za a kashe Naira miliyan 52.3 wajen yin gyare-gyare da kuma kula da tsarin hasken rana na yau da kullum a cikin PHC 34 a fadin jihar.