Gwamnatin jihar Kano ta jajatanwa Iyalan Dan Kasuwar nan Dan Asalin kasar Lebanon kuma Mamallakin Otel ɗin Tahir Guest Palace dake Kano, Mr. Tahir Fadlallah bisa rasuwar sa.
Mukaddashin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan a yau, cikin sakon ta’axiyya da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran sa Hassan Musa Fagge.
Dr. Gawuna ya bayyana matukar kaduwa dangane da samun labarin rasuwar Dan Kasuwar, wanda ya kasance mai kishin jihar Kano da Nigeria baki daya.
Mr. Tahir dai ya samar da ayyukan ci gaba a bangaren kasuwancin Jihar Kano, da kasa baki daya ta fuskoki da dama, baya ga samar da alaƙa mai kyau tsakanin mutanen kasar sa ta Lebanon da kuma Gwamnatin Kano.
A don haka ne mukaddashin Gwamnan a madadin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mika sakon ta’aziyyar ga mutanan Lebanon mazauna Kano, da kuma Yan’uwa da Iyalan mamacin.
Ya kuma bukace su da ci gaba da yi masa addu’a domin rashin sa, rashi ne na mutane da dama, ba iya su kadai ba.
Tare da addu’ar Allah ya gafarta masa zunubansa baki daya.
Yanzu haka dai ana dakon kawo gawar sa zuwa jihar Kano domin binne shi anan, kamar yadda ya bayar da wasiyyar hakan.