Gwamnatin Kano ta shirya ɗaukar nauyin karatun mutum 1001 zuwa Indiya, Uganda
Gwamnatin jihar Kano na daukar nauyin dalibai kimanin 1001 da suka kammala digiri domin yin karatu na gaba da shi a kasashen India da Uganda.
Gwamna Abba Kabir ya kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu na kasashen waje, wanda ya fara da mutane 550 a ranar Alhamis a Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mijina, Surukana, Suna Bani Takaici Saboda Ban Samu Haihuwa Ba, Matar Aure Na Neman Saki
Kabir ya yaba da shirin bayar da tallafin karatu na kasashen waje da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bullo da shi, yayin da ya bayyana alfanun da jihar ke samu daga hakan.
Ya bayyana cewa kokarin da gwamnatin Kwankwaso ta yi ya kasance babban kwarin gwiwa ga gwamnatinsa na ci gaba da hakan.
Mista Kabir ya ce an ga karara cewa wasu daga cikin wadanda Kwankwaso ya horas da su a karkashin shirin a yanzu suna rike da muhimman mukamai a wannan gwamnati.
Kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ibrahm, babban jami’in kididdiga na jihar, Farfesa Aliyu Isa Aliyu da kuma mai ba da shawara na musamman kan kirkire-kirkire, Dr Bashir Muzakkir, da dai sauransu.
Kabir ya ce, “Bari in ce gwamnatin ubangidanmu Sen. Rabiu Kwankwaso ce ta kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu a kasashen waje.
“Mai girma Sanata ya dauki nauyin karatun malamai guda uku zuwa kasashen waje a kusan kasashe 16 a fadin duniya.
“Wannan yunƙuri guda ɗaya da gwamnatinsa ta yi ya samar da ƙwararru da yawa da masu digiri na uku, dubunnan masu digiri na biyu, dubunnan ƙwararrun masana kimiyyar likitanci, injiniyanci, kimiyyar halitta, matukin jirgi, ƙwararrun ruwa, da dai sauransu.
“Kokarin da gwamnatin Kwankwaso ta yi ya kasance babban kwarin gwiwa ga gwamnatinmu wajen ci gaba da wannan manufa mai matukar amfani da kuma shahararriyar manufar bayar da tallafin karatu a kasashen waje.
“A dangane da haka, na yi matukar farin ciki da cewa, wasu daga cikin abubuwan da aka samar a wannan manufar a yau sun mamaye muhimman mukaman gwamnati a wannan gwamnati.”
Tun da farko a nasa jawabin, Kwankwaso ya yaba da kokarin gwamnatin jihar kan yadda ta ci gaba da tafiya a wannan hanya.
Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su tabbatar sun cika burinsu da kuma zama masu amfani ga iyayensu da ‘yan uwansu da kasa baki daya.
A wani labarin kuma:Alkalan Kotun Koli ne za su yanke hukunci kan Atiku, Obi ga Tinubu
Kotun kolin Najeriya ta kafa wani kwamiti mai mambobi bakwai domin sauraron karar da Atiku Abubakar, Peter Obi da Chichi Ojei suka shigar.
Mutanen uku, ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP), da Allied Peoples Movement (APM), suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.