- Gwamnatin Kano ta soke takardar shaidar aiki na dukkan makarantu masu zaman kansu da ke aiki a fadin jihar
- An dauki matakin ne a ranar Asabar a yayin wani taro da masu makarantu masu zaman kansu
- Daukar matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya na aiki a jihar
Gwamnatin jihar Kano ta soke takardar shaidar aiki na dukkan makarantu masu zaman kansu da ke aiki a fadin jihar.
An dauki matakin ne a ranar Asabar a yayin wani taro da masu makarantu masu zaman kansu dake jihar, Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Barno: Kwamishiniyar Harkokin Mata Ta Sha Rantsuwar Kama Aiki, Ta Nemi Wata Bukata
Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan cibiyoyin masu zaman kansu da na sa kai, Alhaji Baba Umar ya bayyana cewa ana bukatar dukkan makarantu masu zaman kansu da su gaggauta kammala yin sabbin rajistar fom, saboda gwamnati ta kaddamar da shirin bayar da sabbin ta kardun shaida.
Umar ya bayyana cewa matakin ya jaddada kudirin gwamnati na ganin cewa makarantu masu zaman kansu sun bi ka’idojin da aka gindaya na aiki a jihar.
“An tunatar da masu makarantu masu zaman kansu alhakin da ya rataya a wuyansu na biyan harajin kashi 10 ga gwamnati. Wannan alƙawarin kuɗi koyaushe yana haɓaka ci gaba a fannin,” in ji shi.
Mashawarcin na musamman ya tabbatar wa duk masu ruwa da tsaki cewa zai tabbatar da gaskiya da adalci wajen kula da harkokin makarantu masu zaman kansu a jihar.
Ya jaddada bukatar aiwatar da ka’idojin aiki ta masu mallakar makarantu masu zaman kansu wadanda suka hada da kayan aiki, yanayin koyo, da’ira, da jadawalin karatu.
Mai ba da shawara na musamman ya kuma tabbatar wa iyaye fifikon da aka ba su wajen kiyaye muradun su da na ‘ya’yansu.
A nasa jawabin shugaban kungiyar masu makarantu masu zaman kansu reshen jihar Kano Alhaji Muhammad Adamu ya yabawa gwamnati bisa wannan matakin da ta dauka, inda ya kara da cewa matakin abin yabawa ne na daukaka bangaren ilimi na cikin gida.
Sannan ya yi kira ga masu mallakar makarantu masu zaman kansu da su hada kai da gwamnati wajen ganin an gudanar da sauye-sauyen, domin an yi hakan ne domin amfanar duk masu ruwa da tsaki.
A yayin taron an fitar da wata sabuwar da’ira da aka kera domin tattara bayanai masu zaman kansu da na sa kai a fadin Kano baya ga raba fom din rajista na sabbin shiga makarantu domin inganta aikin rajista.
A wani labarin kuma,Juyin Mulki: Sheikh Bala Lau, Da Wata Tawaga Sun Isa Nijar Domin Tattaunawa
Wani babban malamin addinin musulunci kuma shugaban kungiyar Jama’atu Izalatu Bidi’ah wa Ikamatus Sunnah, da babbar kungiyar Salafiyya a Najeriya, ya isa jamhuriyar Nijar tare da sauran malaman addinin musulunci na Najeriya, a wani bangare na kokarin diflomasiyya na maido da zaman lafiya a wannan kasa ta yammacin Afirka. Wakilinmu ya tabbatar da hakan a ranar Asabar din nan.
Jaridar PUNCH ta bayyana cewa Lau ne zai jagoranci tawagar malaman addinin musulunci bayan amincewar shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya baiwa malaman damad su shiga tsakani da tattaunawa da takwarorinsu na jamhuriyar Nijar.