Gwamnatin Kano zata baiwa nakasassu tallafin karatu zuwa kasashen waje
Gwamnatin jihar Kano za ta bayar da tallafin karatu zuwa kasashen ketare ga nakasassu a jihar.
Gwamnati ta ce nakasassu za su ci gajiyar shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafin karatu zuwa kasashen ketare muddin sun mallaki abubuwan da ake bukata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Ciyo Bashin Bankin Duniya
Kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
A cewar Kwamishinan, “Yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane dan asalin jihar, daidai da yarjejeniyar kasa da kasa.”
“Tabbas za mu ba da tallafin karatu ga waɗanda ke da digiri na farko da na biyu, gami da nakasassu, don ƙarfafa su su zama ‘yan ƙasa masu fa’ida da rayuwa mai ma’ana.”
Doguwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga jami’an kungiyar Mercy Corps da Coalition of Disabled Self Advocacy Network Group, wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka ziyarce shi tare a ofishin sa.
Ya ce, “Gwamnati za ta kuma duba yiwuwar kafa makarantun da za su hada da su a sassan jihar, duk da cewa za a binciko dama guda 5 don samar da abubuwan da suka dace a makarantun gwamnati da ake da su.
“Wannan shi ne don tabbatar da cewa an shigar da nakasassu a cikin tsare-tsaren ci gaban mu.”
Ya jaddada cewa, a wani bangare na kudirin tallafa wa nakasassu, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta ba su fom din rajistar NECO guda 150, inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da wannan dama ta yadda za a samu ingantacciyar rayuwa.
Kwamishinan ya yi alkawarin cewa, gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu don kyautata jin dadin jama’a, inda ya bukaci abokan huldar ci gaba da su sanya hannu a cikin manufofin gwamnati da shirye-shiryen gwamnati, don tabbatar da sakamako mai dorewa.
A wani labarin kuma:Peter Obi, LP Sun Yi Tsokaci Kan Mukaman Da Tinubu Ke Ba Gwamnonin Wasu Jamiyyar
Jam’iyyar Labour Party (LP) da mai rike da tutarta a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, sun yi kaca-kaca da shugaba Bola Tinubu, kan ba gwamnonin jahohi mukamai, ciki har da wadanda aka zaba a jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da LP.
A wani taron kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a Abuja a daren ranar Talata a Abuja, shugaban kungiyar, Abdulrahman Abdulrazaq ya ce Tinubu ya bukaci taron don ya zabo kwararrun da za su yi aiki a shuwagabanni da hukumomin gwamnatin tarayya da aka rusa a watan jiya.