Gwamnatin Katsina ta baiwa Jami’ar kiwon lafiya mazauni
Gwamnatin Jihar Katsina ta bai wa sabuwar Jam’iar Ilimin Kiyon Lafiya dake Funtua Mazauni.
Gwamnan Jihar ta Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara ga Ministan Ilimi na kasa Farfesa Tahir Mamman, a ofishin sa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ba Tsoron Da Kudu Maso Gabas Za Taji Kan Jagorancin Tinubu – Akpabio
Gwamna Dikko Radda, ya bayyana ma Ministan Ilimi cewa tuni dai Gwamnatin Jihar Katsina ta bada Funtua Technical College a matsayin wurin da za ayi amfani da shi domin fara koyarwa a sabuwar Jami’ar.
Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar Katsina zata cigaba da bada cikakken goyon baya ga Ma’aikatar Ilimi da kuma jami’ar wajen ganin an gudanar da aiki a cikin sauki ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan ya bukaci al’ummar yankin Funtua da su ba da goyon baya da hadin kai domin samun nasarar fara koyarwa a jami’ar.
A nashi jawabin Ministan na Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya bayyana godiyar sa ga Gwamna Radda bisa ga irin yadda ya jajirce da kuma goyon bayan da yake ba Shugabannin wannan jami’a da kuma ita kan ta Ma’aikatar Ilimi, wanda a cewar sa yana bada muhimmiyar gudunmuwa don ganin an samu nasarar kafa wannan jami’a a Funtua, Katsina.