Uwar Gidan Gwamnan jihar katsina, Hajiya Zulaihat Umar Radda ta ce gwamnatin jihar da gidauniyarta ta tallafawa mata za su ci gaba da tallafawa masu cutar sikila
Hajiya Zulaihat ta faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da rabon magungunna cutar sikila ga mata da ƙananan yara a Katsina.
KARANTA A NAN: Babbar kotun tarayya ta sanya ranar da za a cigaba da shari’ar Nnamdi Kanu
Gidauniyar uwar gidan gwamnan da haɗin guiwar ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina ne suka ɗauki nauyin rabon magungunan sikila da na zazzabin cizon sauro.
Uwar gidan gwamna ta yi jawabi mai jan hankali
A jawabinta, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda ta ce:
“Muna godiya ga Allah SWT da ya nuna mana wannan rana wadda nike cike da farin ciki domin kaddamar da rabon magunguna.”
Ta kara da cewa sa hannun gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Raɗɗa ta hannun ma’aikatar lafiya ne ya ƙara farfaɗo da shirin.
Daga nan sai ta ƙara godewa Allah tare da yin alkawarin cewa shirin zai ci gaba ka’in da na’in. Sannan ta kuma roki al’umma da su rika gwaji kafin aure.
Kwamishina ya yabawa matar gwamna
A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar katsina, Dakta Bishir Gambo Saulawa, ya yabawa uwar gidan gwamnan bisa wannan kokari da take yi na tallafawa masu wannan lalura a fadin jihar katsina.
Ya ce gwamnanatin jihar katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda na da kyakkyawan tsari da shiri domin inganta harkokin lafiya a fadin jihar katsina.
KARANTA A NAN: Nine kakanka idan ka dawo APC – Ganduje ya fadawa Kwankwaso
An gabatar da jawabai dangane da muhimmancin taimakawa masu sikila daga bakunan mahalarta taron da suka hada da babban sakataren ma’aikatar lafiya, Dakta Tijjani, shugaban hukumar lafiya a matakin farko, Dakta Shamsu Yahaya da sauransu.
A wani rahoton kuma Mazauna garin Katsina sun koma amfani da keken Shanu wajen jigilar kayan Amarya.
Biyo bayan cire Tallafin Man Fetur da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi, wasu mazauna garin Daura a Jihar Katsina sun koma amfani da Amalanken shanu wajen kai kayan Amarya da sauran wasu kayayyakin
Asali: Dimokuraɗiyya