By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar Legas ta gana da shugabannin kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa reshen jihar a wani yunkuri na dakatar da tafiya yajin aikin gargadi na kwanaki uku da kungiyar ta shirya yi.
Kungiyar NANNM reshen jihar Legas ta kammala shirin fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku a ranar Litinin domin nuna adawa da rashin albashi da yanayin aiki a bangaren kiwon lafiya na jihar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Mista Gbegba Omotoso, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don dakatar da tafiya yajin aikin.
Sannan ya ce, “Gwamnatin jihar ta gana da su, za a sake yin wani taro da yammacin yau Lahadi. Daga abin da na koya, gwamnati za ta kyautata musu kuma za tasa su murmushi.
“Ba mu yi imanin cewa ya kamata a bar wani bangare na fannin kiwon lafiya acikin wani yana yi ba.Za mu ci gaba da haɗa su don kada a sami cikas ga tsarin kiwon lafiya.
“Yayin da muke gina ababen more rayuwa, muna kuma kara karfin ’yan Adam. Mun yi musu yawa ta fuskar horarwa da walwala, sannan idan suka ce wadannan ba su isa ba, mutanenmu ne, za mu saurare su. Za a yi duk kokarin da za a magance matsalolin cikin ruwan sanyi.”
Sai dai sakataren kungiyar ta NANNM, Mista Toba Odumosu, ya ce za a fara yajin aikin ne a ranar Litinin mai zuwa.
“Ba tare da la’akari da ganawar da muka yi da gwamnatin jihar ba, babu yadda za a yi mu dakatar da yajin aikin a yammacin yau (Lahadi). Muna bukatar majalisa ta soke shi kuma ba za mu iya yin hakan ba sai ranar Litinin,” in ji Odumosu.