Gwamnatin jihar Osun ta zargi gwamnatin Gboyega Oyetola da tara basussukan fansho da albashi har naira biliyan 76.
Mai magana da yawun Gwamnan Jihar, Olawale Rasheed, ya rawaito Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar Kudi, Misis Bimpe Ogunlumade ta yi wannan ikirari a lokacin da take yi wa jami’an sabuwar gwamnatin bayani kan halin da kudin jihar ke ciki a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Biden Ya Sha Alwashin Ganawa Da Putin Idan Yana Da Sha’awar Kawo Karshen Yakin Ukraine
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayanin da aka yi ya sabawa ikirarin da tsohon Gwamnan ya yi na cewa ya bar wa sabuwar gwamnati tsabar kudi Naira biliyan 14 da sauran maganganun bogi da a yanzu aka gano cewa karya ce.
Fassarar albashi da kuma kudaden da suka shafi fansho kamar yadda babbar sakatariya ta bayyana kamar haka:
(I) Albashi: Naira 29,875,191,128.64
(II) Bashin Fansho: Naira 45,375,237,693.40
(III) Tsarin Tabbacin Rayuwar Rukuni: Naira 554,644,028.97
Wanda Jimlar ta kai Naira bliyan 75,805,072,851.01
“An shawarci jama’a cewa wannan ba shine jimillar bashin da gwamnatin da ta shude ta bari ba saboda ana ci gaba da yin bayani kan wasu hanyoyin biyan bashin gobe,” in ji gwamnatin.
A wani labarin kuma, IGP Ya Bukaci Kotu Ta Soke Hukuncin Da Ta Yi Masa Na Daurin Watanni Uku
Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya ce ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, inda ya shigar da bukatar a yi watsi da shari’ar rashin gaskiya da kuma hukunta shi.
A cikin karar da aka shigar a ranar Alhamis, Baba ya yi karin haske kan dalilan da ya sa ya kamata a yi watsi da umarnin.
Ya ce ya samu shawarar da ta dace ta fannin shari’a daga kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashin shari’a na rundunar.