By Ishaq Dabai
Gwamnatin rikon kwarya ta Afghanistan, wacce ta kunshi mambobin kungiyar Taliban baki daya, ta gudanar da taron majalisar ministocin ta na farko tun bayan da ta karbi mulki a watan Agusta.
A cewar wata sanarwa da babban mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fitar, yace majalisar ministocin Taliban ta amince a wani taro a Kabul ranar Litinin don sake bayar da fasfo da katunan ID ga ‘yan Afghanistan.
Taron majalisar ministocin ya kuma dora wa gundumar Kabul sabbin hanyoyin da za su bi don hana kwace filaye ba bisa ka’ida ba. An nemi ma’aikatun tsaro daban daban dasu kafa kwamitin hadin gwiwa don inganta tsaro a babban birnin kasar da kuma larduna.
Bayan kifar da gwamnatin Afganistan dake samun goyon bayan kasashen yamma, kungiyar Taliban ta kafa gwamnatin rikon kwarya a watan daya gabata inda ta bayyana Mullah Mohammad Hassan Akhund a matsayin mukaddashin firaminista.
Taliban ta kuma nada sabbin ministoci ga gwamnatin rikon kwarya a ranar Litinin, da kuma sabbin manyan tagulla na sojojin kasar.
A jimilce, an sanar da sabbin nade naden mukamai 38 da babban jagoran Taliban Shaikh Haibatullah Akhundzada yayi, kusan dukkan su malaman addini ne daga kabilar Pashtun, wani abin takaici ga ‘yan Afghanistan dake kira da a kafa gwamnatin wucin gadi ta kabilu da kuma wacce ta hada da mata.
Daga cikin sabbin nade naden akwai karin mataimakin firai minista, Mawlawi Abdul Kabir, wanda kuma memba ne a majalisar shugabannin Taliban kuma wanda ya yi aiki a manyan mukamai a lokacin mulkin Taliban a Afghanistan a karshen shekarun 1990.