- Shugaban Syria Bashar al-Assad ya ba da umarnin karin albashin kashi 100 cikin 100 a fadin kasar
- Karin albashin, wanda ya shafi daukacin ma’aikatan kasar shi ne na tara tun shekarar 2011 lokacin da yakin Syria ya barke
- Hakan ya biyo bayan da gwamnatin kasar ta kara farashin man fetur
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya ba da umarnin karin albashin kashi 100 cikin 100 yayin da gwamnatin kasar ta kara farashin man fetur kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana, Tribune Online ta rahoto.
Karin albashin, wanda ya shafi ma’aikatan kasar, wadanda suka yi ritaya, da na soja, shi ne na tara tun shekarar 2011 lokacin da yakin Syria ya barke.
KARANTA WANNAN: Kasar Jamus Ta Amince Da Shirin Halatta Mallakar Tabar Wiwi
Tun daga lokacin ne tattalin arzikin kasar ya fada cikin mawuyacin hali.
Kafin yanke shawarar, albashin jami’an farar hula na kowane wata ya kasance daga kusan dala 10 zuwa 25 dangane da darajar fam na Syria.
A ranar Talata an farashin ya karu daga Ma’aikatar Kasuwancin Cikin Gida da Kariya ta Siriya na kusan kashi 180% na sufuri da man dizal da kuma kusan kashi 1650% na man fetur octane na yau da kullun.
Direbobin bas da dama ne suka tsallake aiki a ranar Laraba sakamakon karin farashin man fetur, lamarin da ya janyo cunkoso a kan tituna.
Farashin abinci ya karu da kashi 30 zuwa 100 sakamakon karin farashin.
A wani labarin kuma, Wani Gwamna Ya Roki Tsohon dan Majalisar PDP Ya Koma APC
Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya roki tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Sanata Obinna Ogba da ya koma jam’iyyar APC
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jihar a yayin kaddamar da gidan Radiyon LEGACY FM da talabijin
Gwamnan ya kuma yi kira ga tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar da wasu su koma APC.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, a ranar Talata, ya roki tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Sanata Obinna Ogba da ya koma jam’iyyar APC.
Nwifuru ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jihar a yayin kaddamar da gidan Radiyon LEGACY FM da talabijin da tsohon Sanata Ogba ya gina wanda ya wakilci shiyyar Ebonyi ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8 da ta tara 9.