Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen janye ƙarar da ta shigar da Emefiele
Gwamnatin tarayya ta nemi a janye karar ‘mallakar makamai ba bisa ka’ida ba’ da ta shigar a kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da aka dakatar a babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas.
Daraktan shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta tarayya Mohammed Abubakar ya shaida wa mai shari’a Nicholas Oweibo cewa bukatar ta biyo bayan sakamakon ci gaba da bincike da gwamnati ta yi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Nijar: Babu Kokwanto Shiga Tsakanin ECOWAS zai dakatar da juyin mulki a Afirka – Farfesa Akinyemi
Mai shari’a Oweibo ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Alhamis 17 ga watan Agusta, 2023 domin yanke hukunci kan bukatar
A wata hira da ‘yan jarida bayan kammala shari’ar, DPP ta ce an shigar da sabbin tuhume-tuhume 20 a babbar kotun birnin tarayya (FCT) kan gwamnan CBN da aka dakatar.
Ya ce daya daga cikin tuhume-tuhumen ya zargi Emefiele da “ba da damammaki ba bisa ka’ida ba.
A wani labarin kuma:Shugabannin Sojojin Ƙasashen yammacin Afirka sun fitar da ranar da za su tattauna rikicin Nijar
Wasu majiyoyin soji da na siyasa a yankin sun bayyana a jiya Talata cewa, shugabannin soji na kungiyar ECOWAS na yammacin Afirka za su gana a Ghana a wannan mako domin tattauna yiwuwar shiga tsakani a Nijar.
Taron na ranar Alhamis da Juma’a – wanda aka shirya gudanarwa a karshen makon da ya gabata amma daga baya aka dage – ya zo ne bayan da shugabannin ECOWAS a makon da ya gabata suka amince da aikewa da “dakatar da za ta maido da tsarin mulki” a Nijar, wanda aka hambarar da shugaban kasar a ranar 26 ga watan Yuli.