Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana kisan gillar da ‘yan kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) ta yi a matsayin abun ban tsoro da dabbanci, kungiyar wacce ta kasance reshen kungiyar IPOB da ke dauke da makamai suka yi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ministan, ya ba da tabbacin cewa wadanda suka kashe jami’an “ta hanyar cin naman mutane”, da suka yi a faifan bidiyo tare da yada wannan danyen aikin za a gurfanar da su a gaban kotu.
A cewar sanarwar, hari da aka kashe jami’an tsaro wani hari ne da ba za a amince da shi ba a jihar. “Muna da sahihan bayanai cewa ASP Francis Idoko (AP No. 154945); Sufeto Emmanuel Akubo (AP No. 222336) da Insfekta Rufa’i Adamu (AP. 285009) dukkansu jami’an ‘yan sandan Najeriya ne, jami’an tsaro na Eastern Security Network (ESN) sun yi garkuwa da su, bisa umarnin shugabansu. Chinonso Okafor, aka TEMPLE, ranar 27 ga Nuwamba, 2021.
“An kashe biyu daga cikin jami’an, Insifeto Akubo da Adamu ta hanya mafi muni kuma an yi faifan bidiyo da yawo da gawarwakinsu da aka yanke. Shugaban tawagar ESN da suka kashe jami’an biyu daya ne a tawagar ‘GENTLE’.
Sanarwar ta ce “Chinonso Okafor, babban kwamandan ESN mai kula da jihohin Imo da Anambra, da kuma ‘Gentle’ da kuma duk wadan da suka aikata wannan abun kyama, za su fuskanci hukunci cikin gaggawa.”
Mohammed ya ce ci gaba da cewa hare-haren da ESN/IPOB ke kai wa jami’an tsaro da kuma hukumomin gwamnati ya sabawa kiran da aka yi a wasu bangarori na a warware matsalar IPOB a siyasance.
Ya yi mamakin dalilin da ya sa har yanzu masu yin irin wadannan kiraye-kirayen ba su yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa jami’an ‘yan sanda masu hidima ba.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ministan ya jinjinawa jami’an da suka sadaukar da kansu wajen yi wa kasarsu hidima, da kuma dukkan jami’an tsaro da suke yi wa kasa hidima iyakar karfinsu a cikin mawuyacin hali, sai ya miki ta’aziyya ga iyalan jami’an da aka kashe da yin addu’a a gare su