Gwamnatin tarayya ta nada Mrs Christy Uba a matsayin mai kula da Hukumar masu yiwa kasa hidima ta kasa NYSC.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa nadin nata ya biyo bayan sallamar Birgediya Janar M.K Fadah da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ayu: Atiku Bai Goyi Bayan Sake Tsayawa Takarar Jonathan A Shekarar 2015 Ba – Wike
A cewar wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kasa, Eddy Megwa, ya sanyawa hannu a ranar Talata, hukumar NYSC ta ce Uba ta karbi ragamar shugabancin hukumar, kasancewar itace babban darakta a shirin.
Sanarwar ta kara da cewa “Mrs Uba za ta yi aiki a matsayin mai kulawa, har zuwa lokacin da shugaban kasa zai nada babban Darakta.”
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya
Jajantawa Kasar Indonesiya Bisa Mutuwar Da Girgizar Kasa Ta Haddasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bi sahun kasashen duniya wajen aikewa da sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar kasar Indonesia sakamakon mummunar girgizar kasar data afku.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya ce Najeriya ta tsaya tare da su a cikin wannan mawuyacin lokaci da aka rasa rayukan sama da mutane 160, tare da lalata gidaje 2,200 da kuma raba wasu 13,000 da gidajen su a lardin Java ta Yamma na kasar.