Gwamnatin Tarayya tace ISWAP keda alhakin kai hare-hare ga Kiristoci
Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin tayi Allah wadai da kotun wasu Sanatoci guda biyar na Amurka, inda suke kiran Nijeriya ta yi murabus akan cewa ba ƙasa ba ce, saboda zargin kashe kiristoci.
Sanatocin wanda suka yi kiran a cikin takarda da suka aikewa Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antony Blinken, sun yi zargin hana Kiristoci hana su gudanar da addinin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abinda Tinubu ke fama dashi a halin yanzu kan zaɓar Mataimaki a Takarar sa — Akeredolu
Da yake maida jawabi akan wannan zargin a wata tattauanawa Da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a London, Ministan Yaɗa Labaru da Al’adu Alhaji Lai Mohammed a ranar Litinin yace kiran da suke yi ba komai bane illa rashin fahimtar abinda ke faru a cikin Ƙasar.
NAN ta ruwaito cewa Ministan yaje Landan kan wasu harkoki nashi da kuma kiran wasu Kafafen Yaɗa Labaru na Duniya da wasu Ƙungiyoyi.
Ministan yace “zamu sake cewa Najeriya bata da wata doka data hana ƴan Ƙasa su ƙi gudanar da addinin su.
“Ƙasar bata da wata doka data hana yin addini, kuma ba gaskiya bane cewa Najeriya na kashe wani saboda addinin sa.
Ya ƙara dacewa “Babu wani a Najeriya da ake kashewa, amma muna abubuwan da suka jibanci ta’addanci dake faruwa, Kuma ƴan Ta’addan basu duba addini.
“Suna ɗaukar mutane saboda kuɗi, ba tare da duba addini ba, akwai kuma wasu al’amura kan abinda faruwa na cikin gida na shekaru da dama.
“Idan za’a ce ayi ƙididdiga, zan iya faɗar cewa Musulmai da dama da kiristoci suna daga cikin wanda ta’addanci ya taɓa.”
A cewar Ministan, Ƙungiyar dake hari ga Kiristoci itace ISWAP.
Yace Gwamnatin Tarayya ta kai hare-hare na Soji domin Yaƙar su, kuma ana samun nasara.
“Abinda ISWAP ke yi saboda ƙarfin su, shiyasa suke kai hari a coci da Kiristoci domin su haddasa fadace-fadace.
“Amma a matsayin mu na Gwamnati, muna nan muna bin su
Mi istan yace wasu Ƙungiyoyin na sanar da ƙasashen duniya bayanan da bana gaskiya ba domin su samu kuɗaɗe ga masu bada tallafi.