- Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 100 a kasafin kudin shekarar 2024 don shirin ciyar da dalibai
- Wannan tanadin zai zama abin kara kuzari don karfafa halartar makarantu da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta
- Shirin wanda a baya aka dakatar da shi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu zai koma karkashin ma’aikatar ilimi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2024 ya hada da ware Naira biliyan 100 na shirin ciyar da dalibai.
Ya bayyana hakan ne a yayin rattaba hannu kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.
KARANTA WANNAN: 2024: Sama da Nakasassu 4k Za su Samu Fom Ɗin Rajistar Jarabawar UTME Kyauta
Tinubu ya bayyana cewa, wannan tanadin zai zama abin kara kuzari don karfafa halartar makarantu da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Daya daga cikin abubuwan da suka sa a gaba a kudirin dokar da muka zartar a baya shi ne tanadin Naira biliyan 100 na ciyar da yara ‘yan makaranta.
“Na yi imanin hakan wani abu ne mai kara kuzari da zai karfafa shiga makarantu da kuma magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara ‘yan makaranta.
“Zan gana da kananan hukumomi a matakin gwamnatocin Jihohi domin mu hada kai tare da aiwatar da shirin da ya dace,” in ji shugaban.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa kasafin kudin, “Sabunta Fata” an kafa shi ne a kan rage yawan Kudaden da ake kashewa akai-akai, amma kuma a kara yawan kudaden da ake kashewa.
A farkon watan Disamba, Tinubu ya ba da umarnin sake dawo da shirin ciyar da makarantu tare da ba da umarnin sauya shi daga ma’aikatar jin kai zuwa ma’aikatar ilimi.
Shirin wanda a baya aka dakatar da shi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu zai koma karkashin ma’aikatar ilimi, da nufin ba kawai samar da abinci mai gina jiki ga dalibai ba, har ma da karfafa halarta da kuma inganta koyo.
A wani labarin kuma,NASS Za ta Marawa Tinubu Baya Don Aiwatar Da Kasafin Kudin 2024 – Abbas
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya ce majalisar za ta goyi bayan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024
Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Kasa Tinubu ya rattaba hannu kan Kasafin kudin sama da tiriliyan 28
Zamu Yi Duk Mai yiwuwa don ganin Kasafin ya kai ga abin da ake Sa rai ga ‘yan Najeriya
Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya ce majalisar za ta goyi bayan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2024 don ganin ya kai ga abin da ta sa rai ga ‘yan Najeriya.
Abbas, wanda ya kasance a yayin da Tinubu ke rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 a ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, ya ce shugaban kasa a cikin jawabinsa, wanda aka ambata a takaice, ya yi alkawarin samar da ribar dimokuradiyya bisa kasafin kudin 2024 wanda zai aza harsashin sabunta fata.