Gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aiki za su koma tattaunawa mako mai zuwa da nufin kawo karshen rufe jami’o’in da suka dauki lokaci mai tsawo a rufe.
Ministan kwadago da nagartar ayyukan, Sen. Chris Ngige ne ya bayyana hakan a ofishin sa yayin da yake jawabin bude taro tsakanin bangaren gwamnati da kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT) da ke yajin aiki.
Ngige ya ce za a iya kawar da rikice-rikicen bangarori da dama a fannin ilimi, idan har kungiyoyin da ke bangaren suka yi amfani da manufarsa ta bude kofa kamar kungiyoyin kiwon lafiya, wanda ya kai ga zaman lafiyar da ake samu a fannin lafiya a halin yanzu.
A cikin wata sanarwa da mukaddashin shugabar yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar kwadago ta tarayya Patience Onuobia ta fitar, ministar ta bayyana cewa kowa na da muhimmanci a tsarin jami’a.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati na magance duk wasu rigingimun da ke faruwa a fannin ilimi gaba daya, tare da sanin sarai cewa babu wata kungiya da za ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba tare da sauran kungiyar ba.
Ya ce, “Idan kun fito daga kowace kungiya, ba kwa buƙatar yin alƙawari don ganina.”