Gwamnatin Tinubu ba ta da mafita kan matsin rayuwa da ake ciki – Ayodele ya gargadi ‘yan Najeriya
Shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual Primate Elijah Ayodele a ranar Lahadi ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ba ta da hanyar magance tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya.
Primate Ayodele ya bukaci ‘yan Najeriya da su shirya domin fuskantar yanayi mai wahala fiye da wanda ake ciki yanzu.
Ya bayyana cewa kasar ba za ta ci gaba da rayuwa ba tare da karɓar rance ba, kuma hakan zai iya haifar da gazawar Jihohi da dama wajen kasa tafiyar da harkokin ta musamman a Arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Ayodele Oluwatosin Osho ya fitar ta ce tattalin arzikin zai ci gaba da taɓarɓarewa, kuma nan da shekaru hudu masu zuwa Najeriya za ta ci gaba da fafutuka ne kawai domin ganin ta dai-daita.
KARANTA NAN:Ban Gana da Tinubu a Ranar Bikin Cika Shekaru 80 Na Alake Ba – Obasanjo
Haka kuma Shugaban Cocin ya yi nuni da cewa ɗaya daga cikin hanyoyin kawar da matsalar tattalin arziki ita ce ta yaki da cin hanci da rashawa.
Primate Ayodele ya kuma mayar da martani ga kalaman Shugaban Kamfanin BUA na rage farashin siminti zuwa N3000.
A cewar Ayodele ‘’ Ina so in baiwa Ministan kuɗi da Gwamnan CBN shawara cewa babu yadda za a yi Najeriya ta ci gaba da rayuwa ba tare da karɓar rance ba, don haka Jihohi da dama za su durƙushe idan ƙasar ba ta ci bashi ba.
Tattalin arzikin Najeriya yana cikin wani mawuyacin hali, inda yace Gwamnati ba za ta iya samu maganin matsalolin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ba, sai dai yace ƴan Najeriya su ci gaba da shan wahala ne kawai har tsawon wasu shekaru huɗu masu zuwa.
Shugaban kasa yana bukatar aiki sosai a fannin tattalin arziki;
idan ba ka yaki cin hanci da rashawa ba ba za ka iya kawar da tabarbarewar tattalin arziki ba, kuma ban ga hakan zai iya faruwa ba, yayin da tsohon Gwamnan CBN yake zaune zaune abinshi ba tare da ɗaukar matakin Shari’a a kan shi ba.
“BUA cement yace zai sauko da siminti zuwa N3000 shima ban ga yuwuwar hakan ba saboda abubuwa za su yi tsanani”, inji Shugaban Cocin.