Mataimakin zababben shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu za ta yi hulda da kowane jinsi na mutane.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da Wani littafi, wanda Hadiza Bala Usman, tsohuwar manajar daraktar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA), ta Samar, Kuma aka gudanar da Taron a Abuja ranar Asabar.
KU KARANTA: Ranar Ma’aikata: NLC, TUC Sun Yi Allah Wadai Da Matakin FG
A cikin littafin mai suna ‘Stepping On Toes: My odyssey at Nigerian Ports Authority’, Bala Usman ta bayyana irin gogewar da ta samu a matsayinta na ma’aikaciyar gwamnati.
Shettima, wanda yana daya daga cikin bakin da suka halarci bikin, ya yabawa marubuciyar kan yadda ta dauki lokaci wajen rubuta littafin.
Ya ce Yana Mai son tabbatar musu cewa gwamnatin Asiwaju Ahmed Bola Tinubu mai zuwa za ta kasance abokantaka ta kut ga dukkanin jinsi.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Borno ya koka da yadda ‘yan Najeriya ba son karanta litattafai da akan Samar domin su karanta su karu, Amma basa ribatar hakan.
Daga nan sai ya bukaci masu kudi da sauran alumma kan mayar da hankali wajen habbaka dabi’ar karatu.
A wani labarin Kuma: Al-Nassr Na Shirin Daukan Abokin Wasan Ronaldo A Man United
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta bayyana sha’awar sayen dan wasa abokin Cristiano Ronaldo tsohon a Manchester United wato Alex Telles a wannan kakar, kamar yadda Diario AS ya rawaito.
Telles shi ne dan wasa na baya-bayan nan da ake danganta shi da komawa Al-Nassr yayin da manyan kungiyoyin Saudi Pro League suka bayyana tauraron dan kasar Brazil a matsayin zabin da zai iya karfafa zabin su a bangaren a kakar wasa mai zuwa.