Ministan harkokin wajen Uganda na kokarin kwashe ‘yan kasar 275 da suka makale a rikicin soji da ya barke a Sudan, in ji wani babban jami’i a ranar Laraba.
Karamin ministan harkokin wajen kasar mai kula da hadin gwiwar yankin, John Mulimba, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua ta wayar tarho cewa, gwamnatin kasar ta tuntubi hukumar kula da ‘yan cirani ta kasa da kasa don taimakawa wajen kwashe ma’aikata da dalibai da marasa lafiya da ‘yan kasar Uganda da ke kan hanyar wucewa a kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Wata Jiha Zata Karbi Bakuncin ECOWAS Kan Abinci Da Bikin Al’adu
Ya ce akwai ‘yan kasar Uganda 120 da ke aiki a Khartoum babban birnin kasar Sudan, dalibai 116, marasa lafiya 14 a asibitoci, ‘yan kasar 6 a gajeruwar ziyara, sai kuma matafiya musulmi 19 da ke kan hanyar zuwa Makkah na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
“Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tuntubi hukumar ta IOM inda ta bukaci tallafi da taimako don kwashe ‘yan Ugandan da ke son komawa gida,” in ji Mulimba, wanda ya yi wa majalisar bayani kan shirin gwamnati na kwashe ‘yan kasar.
Kasar Sudan dai na ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula tsakanin sojojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces a birnin Khartoum da ma wasu yankunan da ke wajen babban birnin kasar tun ranar 15 ga watan Afrilu, inda bangarorin biyu ke zargin juna da haddasa rikicin.NAN
A wani labarin kuma, FG: Dalilin Da Yasa Buhari Bai Tsoma Baki A Rikicin Zaben Adamawa Ba
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a jiya ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai tsoma baki a zaben gwamna da aka yi kwanan nan a jihar Adamawa ba domin hakkin hukumar zabe mai zaman kanta ce ta daidaita lamarin.
A cewarsa, ba halin Buhari ba ne a yi watsi da cibiyoyin gwamnati.
Comments 2