Gwamnatin Yobe ta mika mata mai yara bakwai da aka yi watsi da’ita ga Gwamnatin Gombe
Daga Muhammad Gambo Damaturu.
Mai baiwa Gwamnan Jihar Yobe Shawara a fannini Addini, Ustaz Baba Gana M Kyari, ya ziyarci Birnin Gombe domin gabatar da aikin Gwamnati.
Ya kai ziyaran ne don gabatarwa Gwamnatin Jihar labarin wata matar da mijin ta ya yi watsi da ita tare da yara bakwai a garin Damaturu.
Bayan bincike, an gano cewa matar ‘yar Gombe ce.
Sakamakon haka ne, Gwamnatin Jihar Yobe, karkashin ofishin Mai Baiwa Gwamnan Jihar Shawara a fannini Addini, ta tallafawa matar da muhalli, kayan abinci, da Tsaro kafin a mika ta ga Gwamnatin Gombe.
A yayin da tawagar Jihar Yobe ta isa Gombe, Sakataren Gwamnatin Jihar Prof. Ibrahim Abubakar Njodi ne ya tarbe su.
Ustaz Baba Gana M. Kyari ya yaba da irin tarba da karancin da akayi masa a lokacin ziyarar.