Daga Muhammad Gambo Damaturu
Kimanin Alarammomi masu Tsangaya da Malamai 300 ne suka hallara a babban Masallacin dake birnin Damaturu a jihar Yobe, domin sauraron jawabai kan muhimmancin katin zabe.
Taron, wanda Ofishin Mai baiwa Gwamnan jihar Yobe shawara kan harkokin Addini ya shirya shi ne domin fadakar da Malaman addinin, muhimmancin mallakar katin zabe da kuma yin zaben ta fuskar addini.
A jawabin sa na bude taro, Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, wanda Sakataren jihar Alhaji Baba Malam Wali ya wakilta, yace akwai bukatar kowa ya mallaki katin zabe.
Yace bai dace, ace jihar Yobe tana karshen baya ba wajen yawan masu katin zaben ba, don haka ya kamata kowa ya fita don mallaka.
Gwamnan ya kara da cewa, sai idan mutum yana da katin zabe ne kawai zai iya zaban shugaban da yake so, don haka ana jan hankalin shuwagabannin addini da su fadakar da mabiyan su don su yanki katunan.
Daga bisani ya godewa Malaman, ya kuma bukaci su kara himma wajen yiwa jihar Yobe da kasar Najeriya baki daya addu’an zaman lafiya.
Da yake jawabi, mai masaukin baki a taron, wanda kuma shine mai baiwa Gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin addini, Ustaz, Baba Gana M. Kyari ya nuna jin dadin sa kan yadda Malaman Addini suke goyon bayan Gomnati a fannoni daban-daban na kawo cigaban jihar.
Ustaz Kyari yace, duk da irin nisan da wasu yankunan jihar Yobe suke da shi, malaman da suke wuraren sun iso wurin taron kafin ma lokacin soma shi, inda yace wannan alamu ne na biyayya da goyon baya.
Don haka Malam Baba Gana M. Kyari ya ja hankalin Gwamnatin jihar Yobe da cewa ta kara himma wajen yiwa malaman duk abun da ya dace da su a Gwamnatance.
Manyan Malamai wanda suka hada da Limamin babban masallacin jihar Yobe, Sheikh Hudu Muhammad Yusuf da Malam Modu Bukar Jumbam, Wakilan hukumar Zabe ta kasa dake jihar Yobe da na reshen hukumar mai lura da kananan hukumomi sun yi bayanai na jan hankali kan muhimmacin yankan katin zabe da kuma tarihin shugabanci a addinin musulunci.
Taron ya samu halartar manyan jami’an Gwamnati, wakilan Sarakunan Gargajiya da sauransu.