Shugaban Kasar nan Bola Ahmed Tinubu ya ce kasancewar gwamnatinsa mai cikakken iko tana sane da matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta magance duk wata damuwa da ‘yan Najeriya ke da ita kan lamarin.
KARANTA WANNAN Tinubu Ya Bayyanawa Hafsoshin Tsaro cewa Akwai Jan Aikin A Gabansu
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Tinubu wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana haka ne a yayin bikin rufe bikin ranar sojojin Najeriya na shekarar 2023 (NADCEL) da kuma cika shekaru 160 na sojojin Najeriya a ranar Alhamis a Ibadan.
Ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na magance duk wata barazana da kuma kula da kalubalen tsaron kasa da ke fuskantar kasar cikin kankanin lokaci.
Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin duk abin da za ta iya kuma kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi damar tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa masu bin doka da oda da hada kan yan kasar.
“Ina tabbatar wa sojojin Najeriya da daukacin rundunar sojin kasar alkawarin da na yi na tabbatar da jin dadin su, kuma zan magance matsalar kayan aiki, rashin isassun kudade da sauran abubuwan da ke kawo musu cikas,” inji shi.
Tinubu ya kara da cewa gwamnatin sa ta samar da wata hanya da za ta magance dukkan kalubalen da sojojin ke fuskanta domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Yayin da yake kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai su guji duk wani abu da zai iya raba kan al’ummar kasar, shugaban ya yabawa sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro.
Jaridar daily Trust ta rawaito cewa Tun da farko, Babban Hafsan Sojojin (COAS), Manji janaral Taoreed Lagbaja, ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da aiki da kundin tsarin mulkin kasar. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Gwamna Aliyu Ya Kullewa Ma’aikatan Gidan Gwamnati Kofa
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto a ranar Alhamis ya kulle kofar gidan gwamnati ga ma’aikatan da suka zo a makare.
An ce gwamnan ya tuka kansa zuwa gidan gwamnati da misalin karfe 8:30 na safe sai dai ya gano cewa yawancin ma’aikatan ba sa ofisoshinsu daban-daban.
Ya hadu da masu aikin goge-goge da shara da ma’aikaciyar jinya daya a asibitin gidan gwamnati.