Biyo bayan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, gwamnonin a dake goyon bayan gwamnan Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba sun kauracewa taron kaddamar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar a hukumance.
Daily Post ta ruwaito cewa, Gwamnonin sun hada da Samuel Ortom na jihar Benue; Seyi Makinde na jihar Oyo; Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu; Okezie Ikpeazu na jihar Abia da shi kanshi gwamna Wike.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tasa Keyar Tsohon Shugaban Guinea Zuwa Gidan Yari
Wasu masu ruwa da tsaki da ake kyautata zaton na goyon bayan Gwamna Wike ne kuma ba su halarci taron kaddamar da Wamitin yakin neman zaben ba, da aka gudanar a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja a ranar Larabar da ta gabata ba.
Sai dai sauran Gwamnonin PDP masu biyayya ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar sun halarci taron.
A WANI LABARIN KUMA: Dalilin Da Zai Sa Zaben 2023 Ya Gudana Cikin Kwanciyar Hankali — IGP
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Kasae nan, IGP Usman Alkali, ya bayar da tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan za ta hada gwiwa da ‘yan uwa jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Alkali, wanda DCP Basil Idegwu, shugaban rundunar ‘yan sandan tarayya ya wakilta, ya bayyana haka a wata tattaunawa kan manufofin tsaro mai taken “2022 General Election wato Babban Zaben 2022: rashin tsaro a matsayin barazana ga kundin tsarin mulki”, wanda Cleen Foundation tare da hadin gwiwar Ford Foundation suka shirya a ranar Larabar nan a Abuja.