Gwamnonin APC sun gana da Buhari kan ɗage ranar zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa
Ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyya mai Mulki ta APC PGF tace zata yi jawabi akan ɗage ranar zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa, bayan taro da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Talata.
Kwamitin Ruƙo da Tsare-tsaren Zaben Shuwagabannin Jam’iyyar APC na Kasa ya ɗage Babban zaɓen daga 26 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga watan Maris.
Kwamitin ya saki sabuwar jadawalin aikace aikacen da zata yi a Babban zaɓen a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Najeriya nada kayayyakin da ake buƙata domin samar da maganin cutar Covid-19 — Masani
A cewar sabuwar jadawalin zaɓen zai fara daga 24 ga watan Fabrairu, da Kwamitocin da zasu yi aiki domin zaɓen Shuwagabanni na Ƙasa.
Sayar da fom na ƴan takara da za’a zaɓa a ofisoshi zai fara daga ranar Laraba, 9 ga watan Maris, za a kammala sai dashi a ranar 11 ga watan Juma’a.
“A matsayin na ƙungiya, mun yi taro a ranar Litinin, kuma mun amince cewa zamu yi taro da Shugaba Buhari a ranar Talata domin cigaba da tattauanawa akan taro na Ƙasa da sauran al’amura” inji Shugaban Ƙungiyar Abubakar Bagudu.