Kungiyar Gwamnonin Arewa, NGF, ta yi Allah-wadai da hare-haren jajibirin Kirsimeti a kan al’umma a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na Jihar Filato.
Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a madadin gwamnoni 19 a sassan arewacin Najeriya a ranar Talata.
Karanta nanTinubu Yayi Allah Wadai Da Kisan Al’umma A Jahar Filato
Ya bayyana hare-haren a matsayin abin zargi da ban tsoro sannan ya jajantawa iyalai da al’ummomin da abin ya shafa da gwamnati da mutanen Filato.
Abin takaici ne jin labarin hasarar rayuka sama da 100 da kuma barnata dukiya da aka samu a lokacin wadannan hare-haren, musamman a lokacin da mutane ke shirin bikin Kirsimeti.
Irin wadannan ta’addanci yana barazana ga hadin kai da zaman tare da yankinmu ya amince da shi.
Dole ne mu ba da fifiko ga zaman lafiya a cikin al’ummominmu. Yanzu, fiye da kowane lokaci, dole ne mu sake tabbatar da aniyarmu ta zaman lafiya da haɗin kai ba tare da la’akari da bambance-bambancenmu ba.
Dole ne mu hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, kuma mu tsaya tsayin daka kan duk wani tashin hankali da rarrabuwar kawuna, Yahaya ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a Gombe ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Ismaila Uba-Misilli.
A wani labarin kumaJam’iyar APC A Jahar Kano Ta Zargi Gwamnatin Jahar Da Tauye Hakkin Kananan Hukumomi
Yahaya ya yaba wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato bisa yadda ya jagoranci al’amuran da suka biyo bayan hare-haren, inda ya ba da tabbacin cewa gwamnonin Arewa sun tashi tsaye wajen ba shi hadin kai domin tunkarar matsalolin da ake fama da su, kuma za su yi aiki tare domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar.
Yahaya ya kuma yaba wa jami’an tsaro da ke aiki a yankin tare da rokonsu da su kara himma wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma ta hanyar sanya ido da kuma daukar matakan gaggawa.