Gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas guda biyar sun gana a gidan gwamnati dake jihar Enugu, Punch ta rawaito.
Gwamnonin, wadanda su ne kungiyar gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas, sun hada Alex Otti (Abia), Farfesa Chukwuma Soludo (Anambra), Francis Nwifuru (Ebonyi), Dakta Peter Mbah (Enugu) da Sanata Hope Uzodimma (Imo).
KARANTA WANNAN: Nan Bada Jimawa Ba Zamu Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro – Lagbaja
Taron na yau shi ne na farko da za a yi tsakanin gwamnonin biyar tun bayan rantsar da sabbin gwamnonin da aka yi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
An tattaro daya daga cikin abubuwan da za su yi fice a cikin ajandar taron shi ne batun zaman gida dole da akeyi a duk ranar Litinin a yankin na kudu maso gabas.
Bugu da kari sai neman bukatar a sako shugaban kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu, wanda ya nemi a sake shi.
Idan dai za’a iya tunawa Kanu ya kasance a hannun DSS tun watan Yunin shekarar 2021.
A wani labarin Kuma, Majalisar Wakilai Ta Gayyaci Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Kan Bashin Ɗalibai
Majalisar wakilai ta gayyaci babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew Adejo da ya gurfana gaban kwamitinta mai kula da lamunin dalibai da manyan makarantu domin bada bayani kan matakan da ma’aikatar da kwamitin shugaban kasa suka dauka kan bada rancen dalibai wajen aiwatar da ayyukan dokar lamunin dalibai.
Wannan kuma shi ne a yayin da Shugaban Kwamitin, Rep. Tersee Ugboh, ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin halartar Babban Sakatare duk da gayyatar da aka aika makwanni 3 da suka gabata, amma ya zabi ya tura daraktan kula da harkokin shari’a a ma’aikatar domin ya wakilce shi wanda a lokacin da aka tambaye shi wasu tambayar ya kasa bada amsarsu.
Ya bayyana cewa sakamakon taron zai baiwa kwamatin cikakken ilimi domin cigaba da gudanar da wani taro kan dokar.
A cewarsa, taron zai ba da damar bayanai daga masu ruwa da tsaki a fadin hukumomin ta hanyar bayanan da aka gabatar kuma za a hada gyare-gyare ga dokar da aka tsara don amfanin dalibai.