Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jajircewarsa na inganta hadin kan kasa a matsayin muhimman abubuwan da ke cikin Ajandar sa ta sabunta yakini.
Matawalle ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da kwalejin tsaro ta kasa Course 32 a wata lacca mai taken karfafa hadin kan kasa don tsaro da ci gaba a Najeriya ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce, barazana ga hadin kan kasa, tsaro da ci gaban kasa, su ne babban abin da gwamnatin shugaba Tinubu ta sa gaba wajen tafiyar da ajandar sa ta sabon yakini.
Ministan ya ce Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro da ake dangantawa da tashe-tashen hankula, bangaranci, ’yan fashi da makami, neman kayyade albarkatun kasa, kabilanci, da rashin yarda da addini da dai sauransu.
Karanta nanZamuyi Taka Tsan Tsan Akan Mafi Karancin Albashi-Majalisar Dattawa
A cewarsa, shugaban kasar ya yi kokari da nufin magance wasu muhimman batutuwan da ake ganin za su kawo barazana ga hadin kan Najeriya, musamman a fannin nade-naden mukamai na siyasa.
Ya kara da cewa shugaba Tinubu ya nuna kudirinsa na hada kan ‘yan Nijeriya baki daya, ba tare da la’akari da kabila, addini ko jam’iyya ba.
Bugu da kari, shugaba Tinubu, a lokacin da yake birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya, ya yi wata ganawa da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, inda ya bukace su da su dawo gida su bada tasu gudunmawar.
Wannan kadan ne daga cikin kokarin da wasu da dama ke yi na dawo da hadin kan kasa a cikin kasar mu Najeriya.
A wani labarin kumaGwamnatin Jahar Kebbi Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafin Abinci Ga Mabukata
Duk da cewa akwai kalubale kamar ta’addanci, ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma tsageru a sassan kasar nan, hade da tasirin cire tallafin man fetur.
Dukkanin ku za ku yarda da ni cewa wannan gwamnati mai ci ta samu nasarori da dama wajen tunkarar wadannan abubuwa ba wai kawai bayyanar kalubalen ba, har ma da tushensu da manufar karfafa hadin kan kasa baki daya domin samar da tsaro da ci gaban Najeriya in ji shi.