Hajj: Wani rukunin alhazan Kwara sun dawo Najeriya
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu alhazai musulmi 269 daga jihar Kwara suka koma Ilorin bayan kammala aikin hajji a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Wannan dai shi ne karo na biyu na alhazan jihar Kwara da suka iso daga aikin hajjin shekarar 2023 a kasar Saudiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN:Majalissar wakilai ta bukaci JAMB data mai rika zana jarabawar sau biyu a shekara
Alhazan sun tashi daga filin jirgin sama na Jeddah a cikin jirgin Air Peace a ranar Laraba, kuma sun isa filin jirgin na Ilorin da misalin karfe 1:38 na rana.
Kimanin mahajjata 3,740 ne suka gudanar da aikin hajjin shekarar 2023 ta hukumar jin dadin Alhazai ta jihar.
Kashi na farko da ya tara alhazai 272 daga jihar, tun da farko sun isa gida a ranar Larabar da ta gabata.
Ana sa ran za a sake komawa gida, domin kuwa hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa an tanadi dukkan wasu tsare-tsare don tabbatar da cewa dukkan dilolin Najeriya masu lasisi za su fara gudanar da zirga-zirgar jiragen su na shigowa Najeriya yadda ya kamata.
A wani labarin kuma:Cire Tallafin mai: Ina nan zuwa da kayan tallafin da zai sanya murmushi ga ‘yan Najeriya -Tinubu
Dangane da wahalhalun da aka samu na cire tallafin man fetur, Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri su yi imani da gwamnatinsa kamar yadda ya yi alkawarin samar da kayan agajin da za su sanya murmushi a fuskar kowa.
Shugaba Tinubu ya amince cewa yana sane da cewa ‘yan Najeriya na fama da matsalar cire tallafin man fetur amma ya tabbatar da cewa wannan tanadin zai amfani ‘yan Najeriya baki daya.