Kasa da mako guda da samun nasarar kammala aikin Hajjin bana a Makkah, rukunin farko na alhazan Najeriya 813 sun tashi daga kasar Saudiyya inda suke kan hanyarsu ta komawa Najeriya.
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa ta shirya tsaf domin fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa gida a ranar Talata 4 ga watan Yuni.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An Kammala Cikakken Bincike Kan Karyar Sakamakon Maki Na Mmesoma – Shugaban JAMB
Sannan ta bayar da tabbacin cewa za ta kammala aikin dawo da alhazan Najeriya nan da ranar 3 ga watan Agusta.
Ba kamar shekarar 2022 ba, lokacin da take da kusan alhazai 43,000 masu aikin Hajji na farko bayan Covid-19, wanda aka bayyana a matsayin “Hajjin gaggawa”.
Hukumomin Saudiyya sun baiwa Najeriya guraben mahajjata 95,000 a bana.
Hukumar NAHCON ta ware guraben aikin Hajji dubu 75,000 ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi daban-daban da suka hada da babban birnin tarayya Abuja, yayin da sauran dubu 20,000 aka baiwa masu gudanar da yawon bude ido masu zaman kansu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa jiragen biyu na kamfanin jirgin saman Saudiyya FlyNas, sun tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdulazziz da ke Jeddah zuwa Sokoto da Legas a yau Talata.
Jirgin na farko wanda ya taso daga Jeddah da karfe 1:55 na rana dai dai da karfe (11:55 na safe a agogon Najeriya) ya dauko alhazan Sokoto 426 tare da jami’i daya.
Jirgin na biyu ya taso ne daga Jeddah zuwa Legas da misalin karfe 5:57 na yamma agogon Saudiyya dai dai da karfe (3:57 na yamma a agogon Najeriya da Nijar) ya dauko alhazan Osun 387 tare da jami’ai biyu, wanda ya kai adadin alhazan zuwa 813.
A halin da ake ciki kuma, wani jami’in hukumar NAHCON, wanda ya yi magana da Tribune Online da ya nemi a sakaya sunansa daga Makkah da yammacin ranar Talata, ya ce duk da cewa jigilar jiragen da ke zuwa gida na iya samun tafiyar hawainiya, hukumar alhazan Najeriya ta kuduri aniyar ganin ta hanzarta bin diddigin jigilar alhazan kasar.
A cewar jami’in, ganin yadda akasarin kasashen ke jigilar alhazai daga Jeddah da Madina, jirage da yawa za su rika tashi daga filayen tashi da saukar jiragen sama kusan a lokaci guda wanda hakan ka iya jawo tafiyar hawainiya.
Ya kara da cewa mafi yawan alhazan Najeriya za su tashi daga kasar Saudiyya ne ta Jeddah, tunda kusan dukkan alhazan Najeriya sun ziyarci Madina kafin a fara aikin Hajji.
Hakan a cewarsa zai sa hukumar ta NAHCON ta fara jigilar maniyyatan ta hanyar mota kafin a kai su Najeriya.
“Mafi yawan alhazanmu, idan ba duka ba, sun ziyarci Madina kafin a fara aikin Hajji. Zai yi wuya a dawo da su can don jigilar jirgin zuwa Najeriya.
“Tafiyar ta wuce sa’oi shida a kan hanya. Jeddah ita ce mafi kyawun zabi a gare mu a matsayin hanyar tashi da alhazanmu,” in ji shi,
Kazalika ya ba da tabbacin cewa NAHCON ba za ta bar komai ba wajen tabbatar da jigilar maniyyatan Najeriya zuwa gida cikin lokaci.
A wani labarin kuma, Abbas Ya Bayyana Manyan Jami’an Majalisar Wakilai Ta 10
Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, a ranar Talatar nan ya bayyana sabbin shugabannin masu rinjaye da mataimaki da bulaliyar majalisar wakilai ta 10.
Shugabannin sun hada da Julius Ihonvbere (APC – Edo, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai), Halims Abdullahi (APC – Kogi) mataimakin shugaban masu rinjaye, Bello Kumo (APC – Gombe) bulaliya, Adewunmi Onanuga (APC – Ogun, mataimakin bulaliyar majalisar.