Hukumar Alhazai ta Najeriya ta bayyana cewa, an tura wasu alhazai masu juna biyu da basu gaza 75 ba zuwa asibitocin kasa mai tsarki na Makkah da Madina, domin samun kulawar gaggawa,Punch ta rawaito
Hakan na zuwa ne a yayin da hukumar ta lura da cewa alhazai da dama sun yi watsi da nasiha da wayar da kan mata masu juna biyu da ke zuwa aikin Hajji.
KARANTA WANNAN: UTME 2023: JAMB Ta Biya Zunzurutun Kudi Biliyan N1.5bn Ga Cibiyoyin CBT
UTME 2023: JAMB Ta Biya Zunzurutun Kudi Biliyan N1.5bn Ga Cibiyoyin CBT
Usman Galadima na tawagar likitocin Najeriya da ke Makkah ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce mata masu juna biyu yawanci ana shawartar su da su guji zuwa aikin hajjin, saboda yanayin motsa jiki.
Ya ci gaba da cewa, daga cikin mahajjata 75 masu ciki, 30 daga cikinsu an kai su asibitocin Madina, yayin da sauran 45 kuma an mika su asibitocin Makkah.
Ya ce: “Mun sami lokuta masu girma na ciki. Mun ga yanayin ciki na watanni bakwai wanda dole ne a shigar da shi. Muna da wadanda aka kai Asibitin Mata da ke Makkah a nan Makka domin karbar su da basu kulawar gaggawa.
“Hakan kuwa ya faru ne duk da kiran da muka yi na taka-tsantsan kan masu juna biyu da ke shigowa Masarautar (Saudiyya).
“Wannan shi ne saboda gajiyar jiki da kuma dabi’ar samun matsalolin da ke tattare da irin wannan.
“Mun ba da shawarar hana mata masu juna biyu zuwa aikin Hajji. Mun samu masu juna biyu da suka zo aikin Hajji. Muna da masu juna biyu da yawa,A madina muna da masu juna biyu sama da 30. A Makka 45”.
Galadima ya kuma koka da yadda wasu alhazai masu fama da matsalolin lafiya musamman ciwon suga da hauhawar jini suka kasa yin tafiya da magungunan su, duk da kokarin da NAHCON ta yi na wayar da kan alhazai.
Ya kuma yi Allah wadai da kame magungunan da hukumomin Najeriya suka yi, inda ya ce idan aka rubuta magungunan, hukumomin Saudiyya ba za su kwace su ba.
Ya kara da cewa: “Mun kasance muna kula da masu fama da rashin lafiya kamar masu ciwon sukari, da hauhawar jini. Wasu daga cikinsu ba sa zuwa da magungunansu duk da ƙoƙarin da muke yi na wayar da kai, Da zarar sun ga magani a cikin fakiti na asali, ba za su ɗauke shi daga gare su ba.
“Amma na fahimci cewa an kwace wadannan kwayoyi a karshen Najeriya, wannan kuskure ne.
“Matafiyi ya kamata ya rika tafiya da magungunansa da zarar an samu takardar magani, da zarar yana cikin fakitin sa na asali. Yawancin su sun zo ba tare da magungunan su ba. Mun ga marasa lafiya da yawa masu hawan jini suna buƙatar shigar da su.”
A halin da ake ciki, Hukumar ta bayyana ta shafinta na Tuwita (@Nigeriahajjcom) a ranar Alhamis cewa an kwashe maniyyata 50,441 zuwa kasa mai tsarki; Maza 30,011 da mata 20,430.
“Daga cikin jimillar mutane 10,947 a yanzu haka suna Madina, yayin da 39,494 aka yi jigilar su zuwa Makkah.
A wani labarin kuma,Koda nasarar Shugaban kasa ko babu, har yanzu Atiku ne abin alfaharinmu – PDP
Shugabannin jam’iyyar PDP a Jada, mahaifar Atiku Abubakar, sun ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben da ya gabata, ya nuna goyon bayan sa a gare su.
Sun bayyana haka ne a yayin wani biki a sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar Yola a ranar Alhamis cewa rashin nasarar Atiku a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu bai shafi goyon bayansu da amincewar su gare shi ba, kuma ya ci gaba da zama abin alfaharin su.