Halin da Ma’aikata suka shiga kan cire tallafin Mai ya sanya mu tsunduma yajin aikin gargadi – Shugaban NLC
Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya Joe Ajaero ya ce yajin aikin Gargaɗi na kwanaki biyu da kungiyar tayi a baya ya zamar masu wajibi ne Saboda fusatar da ma’aikata suka yi akan halin matsin rayuwa da ake ciki a sabili da cire tallafin Man fetur.
Ajaero ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wajen fara wani taro da aka kira da Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Simon Lalong.
Da yake nuna rashin jin dadinsa kan yadda Gwamnati ke tafiyar da shirin bada tallafin rage raɗaɗin, Ajaero ya ce babu ɗaya daga cikin buƙatun da Ma’aikata suka gabatar wa Gwamnati da yi alkawarin biya wanda a halin yanzu ta cika duk da yajin aikin gargadi na kwanaki biyu da suka yi a baya.
Kungiyar kwadago ta ce ba wai Ma’aikata na da sha’awar shiga yajin aikin ba ne, a’a, abubuwan da ke faruwa a ɓangaren kwadago musamman rikicin kungiyar direbobin tituna ta kasa (NURTW) inda ‘yan sanda suka karbe sakatariyar ya haifar da abin da ake so a ɓangaren.
KARANTA NAN:Gwamna Dauda Lawal Ya Samu Nasara A Kotun Daukaka Zabe
Kafin taron ya watse a wani zama na sirri, Lalong ya ce kasar na ganin kalubalen da ke tattare da ayyukan masana’antu da tashe-tashen hankula da suka yi illa ga tattalin arzikin kasar.
Ya ce yana da kwarin gwiwar cewa tattaunawa mai ma’ana da aka fara yanzu za ta kai ga warware batutuwan da ke bisa teburi a yanzu haka.
“Ina matukar godiya da kuma jinjinawa da gagarumar rawar da NLC ke takawa wajen kare hakki da jin dadin ma’aikatanmu. Sadaukarwar ku da ba da gajiyawa sun kasance masu mahimmanci wajen tsara yanayin aiki na gaskiya da haɗa kai, da tabbatar da jin daɗin ma’aikatanmu.
Mun amince da korafe-korafen da ƙungiyar kwadago ta shigar a baya-bayan nan kuma mun himmatu wajen magance su cikin adalci da adalci” inji Minista Lalong.
“Dole ne kuma mu fahimci haƙiƙanin yanayin tattalin arzikin da ke fuskantarmu yayin da muke ƙoƙarin magance matsalolin ma’aikatanmu dole ne mu kula da daidaito, da inganta ci gaban tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai dorewa ga al’ummarmu.
A yau ina kira ga kowannen ku da ya haɗa hannu wajen tattaunawa mai ma’ana wanda zai ba mu damar dinke duk wani gibi da zai iya kasancewa tsakanin muradun ma’aikata da kuma babbar manufar ciyar da tattalin arzikin kasa zuwa gaba”.
“A cikin tsarin hadin kai da kuma himma wajen ci gaban al’ummarmu mu yi amfani da wannan damar wajen saurare da fahimtar juna. A tare, bari mu bincika sabbin hanyoyin sake fasalin dabarun da ke haɓaka yanayin aiki da fa’idodin ma’aikata, yayin haɓaka tattalin arziƙi mai ƙarfi,” in ji Lalong.