Hana Acaɓa: Ana Cigaba da Rikici, bayan Ƙwace Mashina 200 na ƴan Acaɓa a Lagos
Akwai hargitsi, da tashin hankali a Ƙaramar Hukumar Ojo ta Jahar Lagos a ranar Alhamis a yayinda Jami’an tsaro na haɗaka suka je yankin domin tabbatar da Dokar hana Acaɓa.
An gano cewa, ƴan Acaɓa sun hana a kama masu Baburan su.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hajjin 2022: Gwamna Masari ya aika tawaga Saudiya domin kama wa alhazan Katsina Masauki
Jaridar PUNCH ta tattaro cewa a lokacin suka hana a kama mashinan nasu, wasu daga cikin ƴan Acaɓa da Matafiyan da suka ɗauko sun samu raunuka.
“Ko ina ya zama cike da jama’a. Mun hango masu Mashina suna yin baya cikin gudu. Mun ɗauka faɗa ne, sai kowa ya fara gudun ceton rai. Sai daga baya muka gano ashe Jami’ai ne ke kama Mashina,” Inji wani daya shaida lamarin.
A lokacin da aka tuntuɓe shi ta waya, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Lagos Benjamin Hundeyin, ya jaddada cewa babu faɗa a yankin.
Yace a halin yanzu babu wanda aka kashe.
A cewar sa, rahoto daya ce akwai arangama, ba gaskiya bane ba.
Yace “babu faɗa a yankin. Babu fadan Mashina. Abinda ya faru shine ƴan sanda da sauran Jami’an tsaro sun je domin kama Mashina. Kuma an samu nasarar kama Mashina 200.
“Muna kira ga Jama’a su zamo masu bin Doka. Mashinan da aka kama za’a lalata su.
Comments 1