Manajan Darakta na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA, Honarabul Baffa Babba Dan’agundi ya yi Allah-wadai da takun saka tsakanin jami’an sa da wasu sojoji a jihar.
Mummunan lamarin da ya fara a ranar Laraba ya kai ga dabawa wani jami’in KAROTA wuka wanda a halin yanzu yake fama da jinya a asibiti.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai.
KU KARANTA KUMA Hukumar KAROTA Na Cigiyar Wani Dan Adaidata Sahu Da Ya Dauki Kura
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Rikicin ya samo asali ne lokacin da wasu sojoji hudu a kan babur mai kafa uku wato adaidata sahu suka ki yin biyayya ga jami’in kula da ababen hawa a lokacin da yake gudanar da aikinsa a kan titin B.U.K da ke hanyar mahadar Dan, Agundi Junction.
“Wasu daga cikin mutanen mu sun samu rashin fahimtar juna da wasu sojoji a kuma an caka ma wani ma’aikacin mu wuka wanda ya kai ga barkewar rigima amma mun gode wa Allah da taimakon jama’a da suka kawo daukin mutanen mu.
Kamar dai hakan bai wadatar ba, a yau ma sojojin suka sake yin gangami suka koma ofishin mu na Goron Dutse WRECA tare da muzgunawa duk wani jami’in da ke wurin, inda suka lalata mana motocinmu da na jama’ar da ke hannunmu, sannan kuma suka je cike Idi duk a kokarin neman ma’aikatan mu.
Muna Allah wadai da wadannan hare-hare da sabbin sojoji da suka fito da kuma sabbin turawa aiki a Kano suka kai wanda ya zama abu na shekara.
Muna da kyakkyawar alaka da su a jihar kuma muna fatan za su dauki matakan da suka dace don magance wannan matsala.
Muna kuma mika godiya ga ‘yan sandan da suka gaggauta daukar matakin damke wasu daga cikin wadannan sojoji da suka yi kaca-kaca da jama’a da suka yi kokarin ceto mutanen mu daga zaluncin sojojin.
KAROTA za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a cikin jihar kamar yadda dokokin da suka kafa ta suka tanada, kuma za ta kama duk wanda ya saba ka’idojin zirga- zirgar ababen hawa na jihar.
A Wani Labarin Kuma Gawuna Ya Bukaci Al’umma Su Yi Addu’a Domin Gudanar Da Zabe Cikin Zaman Lafiya
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar APC, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da addu’a domin ganin an gudanar da yakin neman zabe da kuma babban zabe mai zuwa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Dan takarar APC ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a Dawakin Kudu yayin da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam’iyyar APC da sauran mazauna kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa na jihar.