Harin Cocin Owo: So ake a raba Najeriya — Inji Ƙungiyar Arewa
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa tayi Allah wadai da kai hari a Cocin St. Francis Catholic, Owo dake Jahar Ondo inda aka kashe mutane da dama, tare da Jikkata wasu masu ibada a ranar Lahadi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na Ƙungiyar ACF Murtala Aliyu ya fitar a Kaduna a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta kama mutane 100, ta tarwatsa wurin shan Ƙwayoyi 14 a Kaduna
Ƙungiyar ACF ta bayyana hari a matsayin cin zarafin Al’umma da dankwafar da kasa, tare da manufar haifar da rashin soyayya a tsakanin mutane.
Ƙungiyar tace waɗanda suka aikata wannan mummunan lamari dole a kawo ƙarshen shi, yana mai cewa dole a gano su a cikin Al’umma.
Kungiyar Arewa tayi kira ga Jami’an tsaro dasu bada fifiko ga kiyaye rayuka da Dukiyoyin ƴan Najeriya, yana mai cewa “rasa rayuwar mutane, rasa ƙasa ne.”
Ƙungiyar ACF ta Kuma yi Allah Wadai da irin kisan wanda ya faru a Masallatai a Zamfara, da Katsina, da Sokoto, da Kebbi, da Jahar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma da Borno da Jahar Yobe a yankin Arewa maso Gabas.