Olukayode Egbetokun, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, ya kai ziyara hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a ranar Talata, inda sojoji suka kai farmaki suka kashe wani sufeto Daniel Jacob a ranar 21 ga watan Nuwamba.
Yayin da yake yin kakkausar suka kan harin, IGP ya bayyana cewa sojoji sun yi kamar ‘yan ta’addar Boko Haram, inda ya yi alkawarin cewa za a shawo kan lamarin, kuma ba za a sake faruwa makamancin haka ba.
Karanta nanSati 1 Da Bayar Da Belin Emiefiele Amma Har Yanzu Yana Gidan Kurkukun Kuje
Egbetokun ya ce,abin takaici ne da bai kamata ya faru ba. Na yi imani wannan zai zama na karshe da abin zai faru a Najeriya.
Wadannan mutane sun zo ne kamar ’yan fashi kuma sun kai hare-hare a cibiyarmu kamar yadda suka kai hari ga ‘yan ta’addar Boko Haram.
Sufeto Jacob Daniel jami’i ne da ke aikin gadi a ranar Larabar makon da ya gabata, a lokacin da aka kashe shi bayan wani farmaki da wasu sojoji suka kai wa hedikwatar, a wani harin da ba shi da tushe balle makama, wanda aka kai ta hanyar da ake kaiwa ‘yan boko haram.
Ina tsakiyar ku yau da yamma don taya ku bakin cikin da kuke da shi,na sami labarin cewa shi ma’aikaci ne da ya jajirce wajen gudanar da aikinsa.
Ya kasance koyaushe yana nuna mafi girman matakin sadaukar da kai ga aiki. Amma abin takaici, mun rasa shi a hare-haren da ba su dace ba kuma na dabbanci.
A wani labarin kumaFiye Da Yara 700,000 Aka Yiwa Rigakafin Cutar Kyanda A Jahar Kwara
Bayan shiru na minti daya na tunawa da jami’in da aka kashe, Egbetokun ya bukaci jami’an da kada su bari lamarin ya sanyaya musu rai.
A nasa jawabin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Afolabi Babatola, ya bayyana cewa,rundunar ta musamman, da ma jihar baki daya, da ta kasance cikin kwanciyar hankali idan ba don wani abin takaici da ya faru a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba ba. , 2023