By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a a karamar hukumar Ihitte Uboma ta jihar Imo.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Barista Festus Okoye, ya fitar a ranar Alhamis, ya biyo bayan rahoton da kwamishinan zabe (REC), Farfesa Emeka Ezeonu, ya bayar cewa Mista Nwokorie Anthony, ma’aikacin jihar Imo ne. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe shi a ofishin hukumar da ke gudanar da atisayen bada katunan zabe na CVR a Nkwo Ihitte (PU 004) da ke mazabar Amakohia (RA 02) na karamar hukumar Ihitte Uboma.
Sanarwar ta kara da cewa tun da farko hukumar ta dakatar da ayyukan na bada katin zabe na CVR a kananan hukumomin Osu da Njaba na jihar saboda rashin tsaro yayin da ake gudanar da atisayen a ofishin hukumar ta INEC a karamar hukumar Oru ta Gabas, Oru ta Yamma, Orlu da Ohaji-Egbema a yankunan kananan hukumomin jihar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta dakatar da ci gaba da gudanar da ayyukan yin rijistar masu zabe (CVR) a karamar hukumar Ihitte Uboma ta jihar Imo.
“Wannan ya biyo bayan rahoton da Kwamishinan Zabe (REC), Farfesa Emeka Ezeonu, ya bayar na cewa a ranar 14 ga Afrilu, 2022, Mista Nwokorie Anthony, ma’aikacin ofishin Hukumar na Jihar Imo ne ke da hannu a cikin ci gaba da gudanar atisayen CVR, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba ne suka harbe shi a Nkwo Ihitte (PU 004) da ke mazabar Amakohia (RA 02) na karamar hukumar Ihitte Uboma.
“Hukumar ta REC ta kuma rawaito cewa, ofishin na jihar na kokarin gano inda sauran ma’aikatan biyu da suka rage a aikin rajistar suke.
“Kafin faruwar lamarin, hukumar ta dakatar da ayyukan na bada katin zabe na CVR a kananan hukumomin Osu da Njaba na jihar saboda rashin tsaro yayin da ake gudanar da atisayen a ofishin hukumar INEC a Oru ta Gabas, Oru ta Yamma, Orlu da Ohaji – Egbema dake Kananan Hukumomin Jihar.
“Hukumar ta mika ta’aziyyarta ga iyalan Nwokorie Anthony tare da addu’ar Allah ya basu ikon hakurin jure rashin. An kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro domin bankado al’amuran da suka haifar da wannan mummunan lamari tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.
“Muna kira ga shugaban kasa da kungiyoyi daban-daban na jihar Imo da kuma duk masu ruwa da tsaki da su kare ma’aikatan hukumar da ke gudanar da ayyukan kasa.
“Kiyayewa da tsaron ma’aikatan na da matukar muhimmanci ga hukumar, musamman ganin yadda aikin rajistar masu kada kuri’a ya wuce ofisoshin jahohinmu da na kananan hukumomin kasar nan, a kokarinmu na yiwa ‘yan Najeriya hidima.”
Comments 1