By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Asabar din da ta gabata ne babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Alkali Baba Usman ya je gudanar da sintiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da wasu manyan jami’ai da nufin tabbatar da ingantaccen tsaro a kan hanyar.
DUBA WANNAN LABARIN: Wata Matar Aure Ta Shiga Hannu A Jihar Sokoto Bisa Laifin Yin Garkuwa Da Wani Yaro Dan Shekara 3
Usman ya tabbatar da cewa akwai isassun mutane da kadarori domin kare rayuka da dukiyoyi a kan babbar hanyar, inda ya kara da cewa a halin yanzu hanyar ta kasance lafiya.
Da yake zantawa da manema labarai, IGP ya ce ya zayyana wasu muhimman wurare da dabaru a kan babbar hanyar wadanda nan da nan aka yi musu katanga tare da tura jami’an rundunar ‘yan sanda ta wayar tafi da gidanka, sashin yaki da ta’addanci, rundunar tsaro ta musamman.
Kazalika yace mun sanya kungiyar ba da amsa ga bayanan sirri, da kuma jami’an Airwing masu kula da jiragen yaki marasa matuki na rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Usman ya kara da cewa, da dabarun da jami’an suka bi wajen gudanar da aikin, za a sake dawo da zaman lafiya.
Ya kuma umurci jama’a da su yi musayar bayanan sirri tare da hukumomin tilasta bin doka don ingantacciyar aikin ‘yan sanda a duk wuraren.
A ci gaba da kokarin kara musu kwarin gwiwa, USamn ya ziyarci jami’an rundunar sojin Najeriya da ‘yan sandan da aka tura zuwa Rijana domin tabbatar da ma’aikatan kamfanin jiragen kasa na Najeriya da ke gudanar da ayyukan gyara ga kociyoyin jiragen kasa da suka lalace da kuma layin dogo a cikin gari.