Harin Kaduna: Amurka ta yi Allah wadai da sace ƴan makaranta
Amurka ta yi Allah-wadai da sace yara ‘yan makaranta a jihar Kaduna.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa, kimanin mutane 200 da suka rasa matsugunansu, wadanda suka kunshi mata, maza da mata ne, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su, a lokacin da suka shiga cikin dazuzzuka domin diban itace a yankunan Gomboru-Ngala da karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
KARANTA WANNAN LABARIN:UNICEF tayi Allah wadai da sace dalibai a Kaduna
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya a shafinta na X ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci sakamako mai raɗaɗi.
“Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan sace ‘yan makaranta da aka yi a Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a Borno.
“Zuciyarmu tana kan iyalan wadanda abin ya shafa. Muna tsayawa tare da ku wajen neman wadanda suka aikata laifin su fuskanci shari’a kuma a gaggauta dawo da duk wadanda aka kama.
“Muna goyon bayan kokarin Najeriya na ganin an sako su,” in ji ta
A wani labarin kuma:Borno, Kaduna: Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-hare, ya bada umarnin kawo ƙarshen sa
Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da munanan abubuwan da suka faru na sace-sacen mutane masu rauni, da ‘yan gudun hijira a jihar Borno da kuma ‘yan makaranta a jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana a jiya Juma’a, cewa da yawa daga cikin wadanda aka sace daga sansanonin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Ngala ta jihar mata ne da maza.