Akalla jami’an ‘yan sanda uku ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin da ya afku a hanyar Kubwa zuwa Zuba, daura da babbar Estate Gwarinpa a Abuja.
Jaridar Daily Trust cewa lamarin ya shafi wasu jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya ta Special Tactical Squad (STS).
Wani ganau mai suna Musa ya shaida wa wakilin majiyar mu cewa hatsarin ya afku ne yayin da daya daga cikin tayoyin motar ‘yan sandan da ke gudu da sauri ta fashe.
Musa ya bayyana cewa, motar ‘yan sanda kirar Hilux ta kauce daga titin ne kwatsam ta shiga magudanar ruwa inda jami’ai uku daga cikin mutanen suka mutu nan take, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
“Ina daf da tsallakawa zuwa hanya ta gaba sai ga motar rakiyar ‘yan sanda a cikin sauri ta rasa yadda za ta yi ta fada cikin magudanar ruwa, inda ‘yan sanda uku suka mutu,” in ji shi.
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce ya samu labarin cewa jami’an na rakiya ne da suka nufi Kaduna domin yin wani aiki na musamman.
Ya kara da cewa wasu jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC da hukumar bada agajin gaggawa ta FEMA sun isa wurin domin kwashe gawarwakin zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, mataimakiyar Sufurtandan ‘yan sanda (DSP), ta bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.
Adeh, yayin da take tabbatar da hakan, ta ce ba ta san adadin wadanda suka mutu a cikin lamarin ba.
“A gaskiya abin bakin ciki ne mun rasa jami’anmu,” Adeh ta shaida wa jaridar Daily Trust.