Hatsarin Mota Ya Hallaka Mutane 7, da Jikkata 5 a Kogi
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa reshen Jahar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutane 7 tare da Raunata mutane 5 a yayin da wasu Motoci guda biyu suka yi hatsari akan Babban hanyar Lokoja-Abuja a ranar Alhamis.
Kwamandan Hukumar na Jahar Kogi Stephen Dawulung ya tabbatar da faruwar lamarin ga Manema labaru a Lokoja a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanwa-Olu ya Ƙaddamar da ginin Ofishin DSS a Lagos
A cewar Kwamandan Hukumar FRSC, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a yayinda Toyota Hiace ta faɗawa Motar Ƙirar DAF a Akpanya kusa a Koton karfe akan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
“a lokacin da motocin suka jame, nan take mutane 7 sun mutu, a yayinda mutane 5 suka samu raunuka.
“Jami’an mu, da suka yi saurin zuwa wurin, sun taimaka wajen kwashe wanda lamarin ya rutsa dasu, musamman wanda suka ji raunuka domin basu kulawar Asibiti.
“Tuni an kai wanda suka ji rauni zuwa Asibitin Koton karfe, inda ake basu magani, an kuma ajiye gawarwakin a wurin ajiye gawa na Asibiti,” Inji shi.
Kwamandan Hukumar ya Shawarci matuƙa dasu guji tafiyar dare da kuma mugun gudu, tare da bin hannun su na hanya.
Comments 1