A ranar Litinin din da ta gabata ne mutane tara suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Kwana Shettu da ke kan hanyar Potiskum zuwa Azare a jihar Bauchi.
Yusuf Abdullahi, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa wasu 13 sun samu munanan raunuka a hadarin.
Abdullahi ya ce hatsarin ya rutsa da tirelar kirar DAF ta kasuwancin danyan mai, mai lamba KTG08XC da wata motar bas Toyota Hiace, ya kara da cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe Tara da Minti 7 na daren jiya Litinin.
Kwamandan sashin ya bayyana direban tirelar mai suna Alhaji Sani Ali, kuma ya danganta dalilin hadarin dagun wuce kima.
“Mutane 22 ne suka mutu a hatsarin motan wanda ya hada da maza 21 da wata budurwa guda daya.
“Mutane tara wadanda dukkansu maza ne sun rasa rayukansu nan take.
“Wasu 13 kuma sun samu raunuka daban-daban kuma sun kasance maza guda 12 da mace daya budurwa” in ji shi.
Shugaban FRSC ya kuma ce an kai wadanda suka jikkata da kuma gawarwakin wadanda suka mutu zuwa Cibiyar kula da Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare domin yi musu magani tare da tabbatar da iyalansu.
Sai dai ya shawarci masu ababen hawa da su kasance masu lura da ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a duk lokacin da suke tafiyar akan hanya.