Wani mummunan hatsari a jihar Anambra ya lashe rayukan mutane uku tare da jikkata wasu bakwai a ranar Juma’a. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Hadarin ya rutsa da mutane 10 da suka hada da maza shida da mata hudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kamfanin Jiragen Saman Biritaniya Ya Soke Tashin Jirgin Daga London Zuwa Abuja
Daga cikin adadin mutane ukun da suka mutu, akwai maza biyu da mace daya, ciki har da wani mai tafiya a kafa.
Da yake mayar da martani kan hatsarin, kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Anambra, Adeoye Irelewuyi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda ya ce, “wani direban wata babbar mota kirar Scania (na kasuwanci) da ba’a tantance ko wanene ba, mai lamba: LSD697YD da direban Mitsubishi mai launin shudi da fari ne suka yi arangama.”
Ya kuma kara da cewa, “Motar kirar L300 (na kasuwanci) mai lamba LEH596XA ta yi hatsarin ne a kan gadar Onitsha ta hanyar Asaba zuwa Onitsha Expressway ranar 28 ga Oktoba 2022 da misalin karfe 10:00 na safe.”
Hukumar ta FRSC ta ce mai yiwuwa dalilin da ya sa hatsarin ya faru shi ne rashin isasshen birki a motar.
Hukumar ta FRSC ta kuma bayyana cewa, tawagar ta daga Sashin Onitsha RS5.31 ta kai wadanda hatsarin ya rutsa da su Asibitin Toronto domin yi wa wadanda suka ji rauni magani.
Ya yin da ya kara da cewa, an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na asibitin.
A WANI LABARIN KUMA: Fargabar Ta Sanya Hana Al’ummar Wata Jiha A Najeriya Shan Ruwan Rijiya Dana Borehole
Gwamnatin jihar Ogun ta roki mazauna yankunan karkara da ambaliyar ruwa ta shafa, da su kauracewa shan ruwan Borehole, da kuma na rijiya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa yankunan da abun ya shafa su. Haɗar da kan iyakokinta na Isheri, Warewa, Magboro, Arepo tare da Kauyukansu daban-daban