An hango tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye a cikin hotunan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a nahiyar Turai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito yadda Atiku ya fice daga kasar ana tsakiyar yakin neman zaben 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Tsaka Da Yakin Neman Zabe, Atiku Ya Shilla Turai
Tafiyar Atiku zuwa kasashen ketare ta janyo cece-kuce daban-daban, inda wasu rahotanni ke cewa ya yi balaguro ne bisa dalilai na lafiya.
Amma Paul Ibe, mai magana da yawunsa, ya ce tafiya ta kasuwanci ce. Yayin da ake ta cece-kuce kan lafiyar sa, tawagar Atiku ta fitar da wasu hotuna.
An ga Hon Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, da Timi Frank, wani na hannun damar dan takarar shugaban kasa tare da shi.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Tisa Keyar Dan Takarar Sanata Na Jam’iyyar LP Gidan Yari
Wata babbar kotu da ke zamanta a Abakaliki a ranar Talata ta tasa keyar dan takarar Sanatan Ebonyi ta Kudu na jam’iyyar Labour, LP, Linus Okorie zuwa gidan gyaran hali.
An gurfanar da Okorie a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da labaran karya, kisan kai, garkuwa da masu safarar miyagun kwayoyi da kuma wasu tuhume-tuhume guda biyu.