A yau Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da mai martaba Sarki Filipe VI a fadar Zarzuela dake birnin Madrid.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja zuwa birnin Madrid na kasar Spain domin ziyarar aiki bisa gayyatar da shugaban kasar Spain, Pedro Sanchez ya yi masa.
Buhari dai yana tare da rakiyar ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed; Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola; Ministan matasa da wasanni Sunday Dare da karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora.
Dukkanin hotunan sun biyo ne ta hannun Bayo Omoboriowo, Mai daukar hoto na musamman ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.