Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a ranar Lahadin nan ya jagoranci tawagar gwamnonin jam’iyyar PDP da suka fusata zuwa jihar Benuwe, inda gwamna Samuel Ortom ya tarbe su.
Bayan Wike da Ortom, sauran gwamnoni a G-5 sune Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Nasarawa Ya ce Yawan Jama’a Ba shi Ne Matsalar Kasar Nana Ba
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Wadannan gwamnonin da abokansu sun fice daga yakin neman zaben Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, inda suka bada sharadin Sanata Iyioricha Ayu ya yi murabus daga mukamin shugaban jam’iyyar na kasa a matsayin sharadin zaman lafiya.
Sai dai Atiku a wata hira da ya yi da Muryar Amurka, ya ce cire Ayu ba gaskiya ba ne a halin yanzu, inda ya bayyana cewa baya cikin rikicin cikin gida a jam’iyyar.
Hotuna
A Wani Labarin Kuma Ministan Harkokin Wajen Kasar Masar Ya Zama Shugaban COP27
An zabi ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry a matsayin shugaban taron COP 27 na Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi (UNFCCC).
Wakilan kasashen sun zabi Shoukry ne a yayin bude taron da aka yi ranar Lahadi a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar.